Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kiyaye Hatsari ta Najeriya ta Tura Jami'ai 35,000 Don sa Ido Akan Tituna


A yayinda bukukuwan salla ke gabatawo, hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya da ake kira FRSC a takaice ta tura jami'ai 35,000 don kula da manyan hanyoyin kasar mussamman a lokacin bikin sallah da za a yi ranar Talata mai zuwa.

Jami'an, da su ka hada da cikakkun ma'aikata da na sa kai tuni suka fara aiki ta hanyar duba lasisin tuki, lafiyar tayu, da hana gudun tsiya, da sauran su.

Hukumar ta ce ta tura jami'an don sa ido a wurare masu cike da hadari 45 a kan hanyoyin kamar hanyar Akwanga-Lafiya-Makurdi, Jos-Bauchi-Gombe, Sokoto-Tambuwal-Jega-Birnin Kebbi, Katsina-Kano-Wudil-Dutse-Azare-Potiskum, Kaduna-Saminaka-Jos, Abuja-Kaduna-Kano, Okene-Ogori-Isua-Owo corridor, Makurdi-Otukpo-Obollo Afor-9th Mile, Asaba-Abraka-Ughelli-Warri , Ibadan-Ogere-Sagamu , Sagamu-Mowe-Lago da sauran manyan hanyoyi.

Shugaban hukumar kiyaye hatsurran Bobboyi Oyeyemi na nuna damuwa akan yadda manyan motoci kan janyo munanan hatsari.

"Fiye da kashi 90% na manyan motocin dake kan tituna a Najeriya sun fi shekaru 20 da kerawa don haka su kan haddasa hatsari," a cewar Oyeyemi.

Sulaiman Danzaki jami'in kungiyar direbobin manyan mota ne, ya yi fashin baki akan yadda motocin ke aiki da kuma yadda ya kamata direbbobi su yi tuki.

Ganganci na daya daga manyan dalilan da kan haddasa hatsari a titunan Najeriya da kuma sanya shingayen 'yan sanda a wuraren ba a tsammanin samun su.

Saurari cikakken tahoton Nasiru Adamu Elhikaya

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG