Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce a shirye take ta bada hadin kai ga masu bincike, biyo bayan kama tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Turai ta UEFA Michel Platini, kasar Faransa na binciken alakarsa da cin hanci da rashawa wajan baiwa kasar Qatar tikitin karbar bakonci wasan kwallon kafar duniya na shekarar 2022.
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce tana sane da rahotanni game da Platini, amma bata da cikakken bayani kan binciken Faransa ba.
A yayin da yake shugabantar hukumar kwallon kafa ta Turai ta UEFA, Platini shine mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, kuma yana da kuri’a kan kasar da zata dau nauyin cin kofin duniya.
Hukumar ta FIFA ta yi alkawarin bada cikakken goyon baya ga jami’an gwamnati na kasashe a duniya ga wadanda suke gudanar da bincike da yake da alaka da harkokin kwallon kafa.
Jami’an hukumar shari’a a Faransa sun ce tsohon Michel Platini, na tsare ne don binciken alakarsa da cin hanci da rashawa wajan baiwa kasar Qatar damar karban bakoncin gasar duniya na shekarar 2022.
Facebook Forum