Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jose Mourinho, A Karon Farko Ya Maida Martani Akan Sukar Da Akayi


Kocin kungiyar Manchester United Jose Mourinho, ya mayar da martani game da wasu maganganu na sukarsa, da wasu keyi kan yadda ya nuna bacin ransa lokacin da danwasansa Marcos Rashford, ya zubar da wata dama a wasan da Manchester United ta doke Young Boys da ci 1- 0, a cikin gasar cin kofin zakarun Turai 2018/19 wanda ya gudana ranar Talata.

Dan wasan Rashford ya yi gaba da gaba da mai tsaron raga na Young Boys, amma ya harba kwallon sama ba tare da ya jefa a raga ba hakan ya fusata Mourinho sosai.

Mourinho ya ce ya shiga damuwa sosai, amma daga karshe ya samu natsuwa bayan da Marouane Fellaini, ya zura kwallo a ragar Young Boys ana daf da tashi a wasan.

Bayan haka Mourinho ya ja hankali, kan yadda ya yi watsi da kwalaben ruwa lokacin da Marouane Fellaini ya jefa kwallon a raga.

Manchester ta samu nasarar tsallakewa zuwa mataki zagaye na gaba da maki 10 a matsayi na biyu daga rukunin. Inda wasu ke ganin sam sam abin da Mourinho ya yi bai can can taba.

Gary Lineker na daya daga cikin wadanda suka soki abinda Mourinhon ya aikata a wasan. Lineker ya ce idan ya ga koci irin haka, wannan shi zai tabbatar masa da cewa yana da tsauri.

Shi kuwa Mourinho ya mayar da martani kan maganganun ya ce zai so ace, ma su sukarsa su karbi aikinsa na horar da 'yan wasa domin suji yadda abun yake.

Ya ce ba kowane koci ba ne zai iya hakuri da wani abin takaicin da ya gani ba, batare da yaji wani abu a jikinsa ko aikata wani abu ba.

Ya kara da cewa a nasa tunanin duk wani kwarararen manaja ba zai iya sukar dan uwansa ba kamar yadda wasu sukeyi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG