Kamar gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari wadda ta ware fiye da nera biliyon 300 domin inganta harkokin ilimi a kasar haka ma wasu jihohin arewacin kasar suka yi.
Alhaji Ado Dan Sudu dake jihar Legas ya bayyana dalilin da ya sa ilimi na bukatar makudan kudade. Yace an samu matsaloli a duk matakin makarantun kasar musamman wadanda suke gaba da sakandare. Duk wani lalaci yana farowa ne daga makarantu.
Son kasa da hada kan kasa to su faro daga makarantu. Nan ne za'a koyas da yara da dalibai.Yakamata a horas da masu tantance ayyukan malamai a makarantu da zasu yi da gaskiya ba aikin rufa rufa ba. Yakamata gwamnati ta sa ido akan gina ilimin firamare da na sakandare sosai domin nan ne ake kafa tushen ilimi ingantacce.
Wani Malam Danladi Aboki yace ba ware kudaden ne matsala ba illa magance yadda za'a kashesu. Misali kashesu akan samar da kayan aiki da tabbatar da biyan hakin malamai.
Jihar Neja na cikin jihohin da suka ware makudan kudade domin ilimi. Jihar ta ware fiye da biliyan biyar domin ilimi. Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello yace ya ware kudaden ne domin makarantunsu suna bukatan kula sosai. Sun zagaye makarantun jihar kaf. Wasu makarantun yanayin da suke ciki nada tada hankali.
Ga karin bayani.