Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Ci Gaba Da Wahalar Fetur Inji Kachikwu


Taron Masu Ruwa da Tsaki akan matsalar karancin man fetur a Najeriya
Taron Masu Ruwa da Tsaki akan matsalar karancin man fetur a Najeriya

Ministan kasa na ma'aikatar man fetur Dr. Ibe Kachikwu ya yi bayani mai daukan hankali a taron masu ruwa da tsaki akan harkokin man fetur a Najeriya game da wahalar mai da kasar ke fama da shi.

Yadda Najeriya ke ci gaba da fama da karancin man fetur ne yasa masu ruwa da tsaki akan man fetur suka yi taro a Abuja, inda karamin ministan man fetur ya fito baro-baro ya ce matsalar ba zata kau ba sai gwamnati ta gyara matatun manta, ta kuma bar 'yan kasuwa su gina wasu sabbin matatu tare da tsame hannunta daga sayo man fetur.

A cewarsa Najeriya zata dade tana fama da karancin man fetur muddin ba a gyara matatun man fetur na kasa ba cikin hanzari tare da ba 'yan kasuwa damar gina sabbi domin a bar kasuwa tayi halinta.

Batun shigo da taceccen mai shine yake jawo matsala, inji Dr. Kachikwu. A yanzu gwamnati kadai ce take shigo da taceccen mai, lamarin da ministan ke gani bai dace ba. Sannan ana zargin dillalan man suma da laifin boye man fetur don samun kazamar riba.

Aminu Abdulkadir shugaban kwamitin amintattu na kungiyar dillalan man fetur ta kasa yace tsakanin watan Nuwamba da Disamba basu kawo man da suke shigo da shi ba saboda tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya, lamarin da ya kawo rata a tsakanin farashin da suke sayar da mai din a cikin gida da farashin da suka sayowa.

A cewarsa, matatar mai ta kasa wato NNPC, ta gaza kawo daidaito domin a karesu daga yin hasara. To sai dai a nata bayanin, ma'aikatar man tace ta kama wasu gidajen mai na jabu guda biyar a Abuja kana ta yi awon gaba da motoci fiye da dubu hudu shake da man fetur.

Mekanti Kachalla Baru, shugaban NNPC ya bayyana matakan da aka dauka akan kamun da suka yi. Da cewa shugaban kasa ya basu umurni su yi amfani da dokokin hana yiwa tattalin arziki zagon kasa. Dokokin kuma suka yi amfani da su akan wadanda aka kama da laifin boye mai.

Misali, duk gidajen da suka ki sayar da mai an tilasta musu da sayarwa. Suma masu sayar da man da tsada an kwace daga hannunsu an rabawa jama'a kyauta. Daya daga cikin abubuwan da ake bincike shine batun cire tallafi ko a'a da gwamnati tace ta yi.

Sanata Kabiru Garba Marafa yayi karin haske akan kudaden da ake ba manyan 'yan kasuwa su shigo da man fetur. Yace an ba 'yan kasuwa dala biliyan uku da miliyan dari uku su shigo da mai akan farashin dala na gwamnati. Ana sayar da dala N360 a waje amma su ana basu akan N305, inji Sanata Marafa. Alkalumma sun nuna 'yan Najeriya na shan litar mai miliyan 40 a kowace rana.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG