Yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben da aka gudanar a karshen makon jiya a Jamhuriyar Nijar, bayanai na nunin dan takarar jam’iyyar PNDS mai mulki Bazoum Mohamed ne ke kan gaba, yayin da Mahaman Ousman na jam’iyyar RDR Canji ta ‘yan hamayya ke bi masa, lamarin da ya sa kowanne daga cikin bangarorin siyasar kasar ke ikirarin shi zai yi nasara.
Alkaluman da hukumar zabe ta wallafa a shafinta na internet na nunin har ya zuwa karfe daya na ranar Laraba, hukumar ta CENI ta kammala tantance sakamakon da suka shigo mata daga da’irori 69 cikin 266, abinda ke nunin dan takarar jam’iyya mai mulki Bazoum Mohamed ne ke kan gaba da kuri’u 293,739, sai Mahaman Ousman na jam’iyyar RDR Canji mai kuri’u 140,676.
Da ya ke bayyana matsayin jam’iyyarsa ta PNDS Tarayya, Tahirou Garka memba a kwamitin yakin zaben jam’iyyar, ya ce ya na da kwarin guiwar su zasu lashe zaben.
Sai dai ‘yan adawa a ta bakin kakakin jam’iyyar Moden Lumana Bana Ibrahim na cewa, muddin aka bayyana sakamakon kuri’un da ‘yan kasa suka kada na ranar Lahadi 27 ga watan Disamba ba wata tantama dan takarar RDR Canji ne zai yi nasara.
A sanarwar da suka yada a kafafen sada zumunta a yammacin ranar Talata, ‘yan hamayya sun yi kashedi ga jam’iyyar PNDS mai mulki da ta dakatar da abinda suka kira take-take mai kama da yunkurin murda sakamaon zaben.
Yanzu haka hukumar CENI na ci gaba da tattara sakamakon zaben da ke fitowa daga sassa daban daban na kasar, inda ake a wuni na uku na zaman da ta ke yi a cibiyar da ta kafa a Palais des Congres da ke birnin Yamai, inda bayanai ke shigowa sannu a hankali wadanda jami’ai ke gudanar da aikin tantancewa kafin a bayyana su a kafar Telabijin mallakar gwamnatin Nijar, yayin da jama’a ke ci gaba da harkokin yau da kullum hankali kwance.
Saurari rahoton Souley Barma: