Na Ikara ya gamu da ‘Dan Iya inda yace masa, ‘dan uwa ina ka nutse ne naji ka shiru? Ai kwana biyu na ringa neman ka har majalisar ku ta masu zaman zuru.
‘Dan Iya yace, bari kawai ‘dan uwa kasan bana mu ta waru, saboda addu’o’in da muka dinga kan harkar zaben kasar mu ta gyaru, yanzu dai kaga babu murdiya da sibar na baryin kuri’u domin Jega ya riga ya jijjige jimurun jagwalgwala zabe daga wasu tsiraru, saboda har aka kammala zabe babu wani gurbin da aka baiwa tsageru, don kuwa talakawa sun riga sun gane cewa yanzu fa lalle sune dakaru da ka iya kawo sabon salon sauyi tun daga farfaru, shiyasa kaga ‘yan zari ruga da masu zaman zunguro zullumi sunyi shiru.
‘Dan Iya ya cigaba da cewa, kai bari in gaya maka gaskiya na Ikara, wannan karon kowa fa ya taka gagarumar rawa, saboda naga yadda talakawa suka tsaya tsayin daka cikin nutsuwa, suka nunawa duniya suma fa Allah yayi musu wata baiwa, ta yadda suka tunbuke gwamnatin data kwashe shekaru don dasa sabuwa, shiyasa nake murna don dole ne wannan gwamnatin tayi da talakawa, idan ko ba haka ba ta za’a gamu da sabuwar adawa, don kasan talaka ya fiya gaggawa yanzu kowa ya kosa a fara bukin kaukawa, saboda mu yanzu mun sa a ranmu babu wata makawa cewa da zarar sabuwar gwamnati ha hau fa zamu ga sabuwar rayuwa.
Na Ikara yace ehh ‘Dan Iya duk dayake maganar ka gaskiya ce amma yana da kyau kasan fa anyi wasu kurakurai, saboda ko banda matsalolin zaben da aka samu tun a wurin tsare tsare, wasu masu zaben da suka fita fagen kada kuri’ar su sun nuna banbancin yare, wasu kuma suka samu kunnen ‘yan uwansu da magoya baya suka hure, yayin da su kuma matasa suka dinga sare sare masu magudin zabe kuma sun dunga yunkurin buga zure, a wasu guraren kuma haka aka dinga zabe mutane na kan layi har zuwa cikin dare, wannan ne ma yasa dole wasu masu uzuri suka ranta ana kare. Shiyasa nake ganin duk da kuna murna wai ta ‘bare to dole ne mu fara duba da guraren da aka tafka kuskure.
‘Dan Iya eh na yarda da kai amma dole nima ka yarda dani don kuwa ko babu komai mun tsallake duk kanin tsanani, musammam ma yadda wasu ke ta tunani cewa zabe akasarmu zai yi matukar muni, har takai ga wasu sun tattara ‘yan uwansu da dukkanin inasu inasu suka gudu birni, amma sai gashi anyi sa’a Allah ya kawo sauki da salama cikin wannan sha’ani, ta yadda zaben kasar ya ‘dauki sabon launi inda takai ga wanda ke fafutukar adawa ya lashe zabe akusan kowanne fanni, shikuma wanda ke kan madafun ikon da aka kayar ya zama zakara a wannan ‘karni, don kuwa da jin ya fadi ya kira wayar wanda ya kada shi don taya shi murna, wanda wannan ne ya murkushe dukkanin gurnani.