Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton za ta tafi wasu kasashen Afirka uku don tattaunawar cinakayya, da cigaba da kuma matsalolin tsaro.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka t ace Clinton za ta ziyarci Zambia, da Tanzania da Ethiopia bayan ziyararta zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa inda za ta mayar da hankali kan rikicin Libiya.
An shirya Clinton za ta halarci wani taro kan cinakayya na Ministocin Afirka Kan Cigaban Afirka Da Irin Abubuwan Kawo Cigaba Da Ke Nahiyar a Zambiya ran Jumma’a mai zuwa wato 10 ga wannan wata na Yuni ta kuma gana da Shugaban Zambia Rupiah Banda.
A Tanzania, inji Ma’aikatar ta Harkokin Wajen Amurka, Clinton za ta bayar da misali da kasashe biyu da suka amfana sosai da aikin hadin gwiwa da Amurka, ciki har da jerin aikace-aikace.
Clinton na kuma shirin ziyartar kungiyar Tarayyar Afirka a yayin da ta je kasar Habasha ta kuma gana da Ciyaman din Kungiyar Tarayyar Afirka din Jean Ping.
A lokacin wannan balaguron nata, Clinton zata gana da Firayim Ministan Habasha Meles Zenawi da shugaban Tanzania Jakaya Kikwete.