Wani binciken Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa wayar tafi-da-gidanka na iya kara kasadar kamuwa da cutar ‘cancer’ ko daji.
Binciken na Cibiyar Nazarin Cutar Cancer A Duniya ta Majalisar Dinkin Duniya (IARC a takaice) ta sce yakama a bayyana wayar tafi-da-gidanka da cewa ta na iya haddasa cutar cancer – wanda hakan ya sanya na’urar cikin rukuni guda da maganin kashe kwari na DDT da hayakin injin mai amfani da man fetur da kuma coffee.
Hukumar ta IARC ta fadi cikin wata takardar bayanin da ta fitar jiya Talata cewa amfani da wayar tafi-da-gidanka na kara kasadar kamuwa da glioma, wadda cutar cancer c eta kwakalwa, ta kara da cewa yakamata masana su sa ido sosai ko sa gano wata dankataka tsakanin wayar tafi-da-gidanka da yiwuwar kamuwa da cutar cancer.
An maimaita maganar shugaban hukumar Christopher Wild na cewa yakamata nan gaba a yi bincike mai zurfi game da yawan amfani da wayar tafi-da-gidanka na lokaci mai tsawo. Kafin a sami sakamakon, y ace, yakamata a dau mataki daidai ruwa daidai gari don rage fuskantar hadarin wayar tafi-da-gidanka, ciki har da na’urorin amfani da wayar ba kai tsaye ba da kuma yawan rubuta sakonnin da hannu.
Majalisar Dinkin Duniya t ace a yanzu yawan wayoyin da ake amfani da su sun kai kimanin miliyan dubu biyar a duniya, kuma ana cigaba da samin karin masu amfani da wayoyin, musamman ma tsakanin baligai da yara kanana.