Hatsarin kwale-kwale a gabar tekun babban birnin Angola, Luanda, ya hallaka akalla mutane 6 ciki har da yara 2, a cewar hukumomin ‘yan sanda da na bada agaji, a yayin da ake ci gaba da aikin ceto a yau Litinin.
Jirgin ruwa mai dauke da fiye da mutane 30 na cikin tawagar jerin gwanon jiragen ruwan mabiya darikar Katolika dake balaguro a kasar dake shiyar kudancin Afirka lokacin da ya nutse kusa da tsibirin Luanda a ranar Asabar din da ta gabata, a cewar ‘yan sanda.
Kakakin rundunar ‘yan sandan kasar Hermenio Cazacuto ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar mutane 6 sun mutu kuma an yi nasarar kubutar da wasu 17.
Mutane 4 na kwance a asibiti cikin mawuyacin hali sannan wasu 3 sun bata, kamar yadda ya bada karin bayani, inda yace ana ci gaba da kokarin lalubo mutane a yau Litinin.
Al’amarin ya faru ne kimanin mil 2 kusa da gabar ruwan birnin dake bakin teku.
Kakakin hukumar bada agajin gobara Maina Panzu ya shaidawa AFP cewa 2 daga cikin mutanen da suka mutu yara ne masu shekaru 4 da 6.
Ba a kai ga tantance musabbabin afkuwar hatsarin ba, a cewar Panzu sai dai ana zargin sakaci daga bangaren direban jirgin ya haddasa hatsarin, inda yace shima direban ya bata.
Wata kafar yada labaran kasar “Angola24horas” ta bada rahoton cewa kwale-kwalen na dauke da fasinja fiye da kima kuma hatsarin ya hada da wani jirgin kamun kifi da “igiyoyin ruwa da dama”
A sanarwar da ya fitar a jiya Lahadi, shugaban kasar Angola Joao Lourenco, ya aike da sakon ta’aziyyarsa ga” iyalan da mummunan hatsarin ya shafa kai tsaye.”
Dandalin Mu Tattauna