Sarkin Gobir na garin Gatawa Alhaji Isa Muhammad Bawa ya rasu a hannun ‘yan bindigar da suka sace shi bayan kwanaki 25 da suka yi garkuwa da Sarki Bawa da dansa da wani dan uwansa a watan Augusta
A watan Satumba Allah ya yi wa Hajiya Binta Dada Musa ‘Yar’adua, mahaifiyar tsohon Shugaban Najeriya, marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua, cikawa ranar Litinin da karfe 8 na yamma agogon Najeriya, a Asibitin Koyarwa na Katsina.
Ta rasu ta na da shekaru 101 a duniya.
A farkon shekarar 2024, Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya dakatar da Ministar agaji da Walwalar Jama'a, Betta Edu nan take.
Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne domin ba da dama ga hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gudanar da bincike a kanta.
A watan Maris ne 'yan bindiga su ka yiwa makarantar firamare da ake kira LEA Primary School Kuriga 1 kawanya, inda su ka kora daliban makarantar 'yan tsakanin shekaru 7 zuwa 15 da daya daga cikin malaman makarantar zuwa daji.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya ce dalibai 137 aka sace yayin da ya karbi daliban bayan kwashe kwanaki 16 a hannun 'yan-bindigan.
A watan Nuwamba Fadar Shugaban kasa ta sanar da mutuwar Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja bayan wata gajeruwar jinya a Legas ya na da shekaru 56.
A watan Agusta rikici ya barke tsakanin Bobrisky, VDM da Jami'an Tsaron Gidan Yarin Najeriya da hukumar EFCC masu yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa.
Bobrisky ya yi zargin cin hancin a cikin wani faifan bidiyo da wani mai gudanar da jaridar intanet, Martins Otse da aka fi sani da VDM, ya saki a kan wani babban jami’in hukumar gyaran halin Najeriya.
Bobrisky ya kuma yi zargin baiwa jami’an hukumar EFCC cin hancin Naira miliyan 15 domin su daina tuhumarsa da laifin halasta kudaden haram.
A shekarar 2024, tashar wutar lantarki ta kasa ta rugujw karo 12.
A watan Oktoba Isra'ila ta sanar cewa ta kashe shugaban Hamas, Yahya Sinwar, wanda shi ake zargi da kitsa harin ta'addancin da ya faru a ranar 7 ga Oktoba, 2023, wanda ya janyo rikicin Gaza.
Hakazalika, a watan Yuli kasar Iran da kungiyar masu fafutuka suka sanar da rasuwar shugaban Hamas Ismail Haniyeh, jim kadan bayan halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar,
Haniyeh ya shugabanci Hamas tun shekarar 2017.
A watan Satumba, Isra’ila ta sanar da cewa ta kashe jagoran Hezbollah, Sayyed Hassan Nasrallah, wanda ya jagoranci kungiyar da ta kwashe gwamman shekaru ta na rikici da Isra’ila, da kula da sauya sigar ta zuwa wata rundunar dakarun soji da tayi karfin gaske tsakanin fitattun yankunan Larabawa a tsawon lokaci, da ke samun goyon bayan Iran.
A watan Nuwamba kuma shahararren furodusan waka a Amurka Quincy Jones ya rasu yana da shekaru 91.
Jones ya kasance furodusan da ya samar da kundin wakoki na Michael Jackson mai suna “Thriller” wanda ya kafa tarihi.
A watan Disamba tsohon Shugaban Amurka na 39, Jimmy Carter ya mutu yana da shekara 100 a gidansa da ke tsaunin Plains da ke jihar Georgia
An zabe shi a matsayin shugaban Amurka a shekarar 1976 ya kuma hau karagar mulki a shakar 1977 zuwa 1981.
Ga sauran labaran a bidiyo da Yusuf A Yusuf ya hado mana:
Dandalin Mu Tattauna