A lamari na farko, wani Bafalasdine dake dauke da wuka ya soki Yahudawa biyu a wani ofis a birnin Tel-Aviv, kamin mutane su kama shi, daga bisani suka dankashi ga 'Yansanda kamar yadda shaidu suka ce.
Daga bisani a jiyan, an shaida mutuwar wasu mutane uku, an tabbatar da daya daga cikinsu a zaman Bayahude, dayan kuma wanda ya kai harin, a wasu harbe harbe da aka yi da kuma wata mota kusa da wani sansanin 'yan share wuri zauna a kudancin birnin Kudus. Wasu mutane kuma sun jikkata.
Ahalinda ake ciki kuma,yau Jumma'a Amurka zata saki Jonathan Pollard wanda Amurka ta daure kan zargin yiwa Isra'ila leken asiri, amma burinsa na tafiya Isra'ila zai fuskanci jinkiri.
Pollard dan shekaru 61 da haifuwa, wani tsohon ma'aikacin rundunar sojin ruwa ta Amurka a an yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai ne a shekarar 1987, bayan da ya amsa laifin sayarwa Isra'ila bayanan sirri.