Shugaban Amurka Barack Obama da Firayim Ministan Israila Benjamen Netanyahu sun gana a wani sabon yunkurin lalubo bakin zaren kawo karshen rikicin Gabas ta Tsakiya.
Shugabannin biyu sun gana ne a Fadar White House a nan birnin Washington DC inda Firayim Ministan ya sake jaddada rashin goyon bayansa da yarjejeniyar nukiliya da kasar Iran.
An cimma yarjejeniyar ce tsakanin Amurka da wasu manyan kasashen duniya biyar da ita kasar Iran. Israila ta ki kememe ta amince da yarjejeniyar.
Yayinda suke cigaba da ganawa shugaba Obama yace zasu tattauna akan abubuwa da dama da suka hada da kungiyoyin ISIS da Hezbollah da ma wasu kungiyoyin 'yan tawaye da suke kai hare haren ta'adanci.
Duk da banbancin da suke dashi Amurka ta dukufa akan tabbatar da tsaron Israila abun da shi ma Netanyahu ya tabbatar. Ya amince Amurka tana goyon bayan Israila a koyaushe kuma a kowane hali.
A can kasar Jordan kuma wani jami'an sojan kasar ne ya harbe Amurkawa biyu da kuma wani dan Afirka ta Kudu jiya Litinin kafin daga bisani ya kashe kansa.