Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Muna Binciken Dalilin Mace-macen Kano: WHO


A Najeriya, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da wasu gwaje-gwaje a cikin jihar Kano, domin gano ainihin musabbabin mace-mace da ake samu a cikin 'yan kwanakin nan.

Shugaban Najeriya ya ce, da shi da gwamnatinsa suna tare da al’ummar jihar Kano. kuma zai yi iya kokarin sa don ganin an taimaka jihar.

Najeriyar ta shiga makonni kenan a yakin take na annobar COVID-19, a farkon wannan shekarar, ya zuwa yanzu kusan cutar ta yadu a cikin kowace al'umma a duniya.

A farkon wannan watan babban darektan shirin hukumar Lafiya ta duniya wato WHO,Dr Mike Ryan ya bayyana a fili cewa “Afirka ta na kan gaba” a yakin da muke da annobar coronavirus.

A cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman na Shugaban Kasa a kan sha'anin watsa labarai Garba Shehu ya fitar, Dr. Ryan ya ce, "Mun kuma sani cewa akwai karancin kayan aikin kariya a duniya, kayan gwajin kwayar cutar da sauran na’urorin kiwon lafiya da ake bukata don yaki da wannan cutar".

"Ya zuwa yanzu ana hasashen cewa yawan mace-macen da ake yi a jihar Kano sakamakon COVID-19 ne, wannan zai haifar da babban kalubale, kuma matakin da yafi dacewa shi ne gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar suyi aiki kafada da kafada domin nemo mafita" a cewar sanarwar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG