Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CORONA: Amurka Za Ta Taimakawa Najeriya


Buhari Trump
Buhari Trump

A daidai lokacin da ake samun sababbin kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya, Amurka ta ce za ta bayar da tallafin na'urorin numfashi ga kasar domin kula da wadanda suka kamu da cutar.

"Na tattauna da Najeriya a yau" in ji Shugaban Amurka Donald Trump, "su ma su na matukar bukatar kayayyakin na numfashi, kuma za mu aika a kalla na'urorin numfashi 200 zuwa Najeriya, ko ma abin da ya fi haka", Trump ya fada a fadarsa ta White House.

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari a jawabin da ya yi wa 'yan kasar a ranar Litinin, ya bayyana dokar hana shiga da fita a jihar Kano, sakamakon yawan mace-macen jama'a da ake samu, duk da yake hukumomi na musanta alakar su da COVID-19.

To sai dai Buhari ya ce a hankali za'a sassauta dokar hana zirga zirga da aka kakaba a Abuja da jihohin Legas da Ogun.

A jawabinsa da yayi wa kasar, Shugaba Buhari ya ce, ya dau wannan matakin ne bayan nazari da yayi akan dokar da ta dau makwanni 4, domin ba tattalin arzikin kasar damar sake farfadowa sannu a hankali, yayin da ake ci gaba da dakile yaduwar kwayar cutar.

Ya kara da cewa, za'a aika da karin jami’an lafiya da kayayyakin jinya a jihar ta Kano dake arewa maso yammacin kasar, inda zata kasance cikin wannan dokar hana fita saboda karuwar cutar ta COVID-19 a jihar.

A halin da ake ciki, Najeriya na da adadin masu dauke da cutar 1,273 yayin mutum 40 suka mutu asanadiyar cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG