Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Gwamnatin Najeriya Ba Ta Tuntubi Iyayen Dorcas Maida Yakubu Ba


Yau kwana uku ke nan da kungiyar Boko Haram ta fitar da wani faifan bidiyo da ya nuna kimanin ‘yan matan sakandaren Chibok hamsin da suka sace har yanzu suna da rai, kuma kawo yanzu, gwamnatin Najeriya bata tuntubi iyayen yarinyar da tayi magana a hoton bidiyon ba.

Rashin tuntubarsu, ya sake jefa dangin 'yan matan Chibok tunanin an sake yin watsi dasu.

Babu wanda ya tuntubemu. Kila saboda da mu talakawa ne, ko kuma bamu da albarkatun mai a Chibok. Mu ba komi bane. Amma ina farincikin sanin cewa, Allah ya amsa adu’ata ya kare ranta.” Inji Esther Yakubu. ‘Sakon da nake da shi ga gwamnatin tarayya shine, ta saki mayakan, domin sauran mayakan su saki yammatan.”

A cikin faifan bidiyon na baya bayan nan, Dorcas Maida Yakubu, ‘yar Esther Yakubu, ta yi Magana da harshensu tana cewa.

“Muna wahala a nan, Babu irin wahalar da bamu gani ba”. Ku gayawa gwamnati ta basu mutanensu, domin muma mu dawo gida mu zauna daku…babu wani abinda ku, ko mu, zamu iya yi a kan wannan, sai dai kawai a basu mutanensu, domin muma mu tafi gida.

Dorcas Maida Yakubu ta kuma ce, an jiwa da dama daga cikin wadanda aka kama rauni, an kuma kashe wadansu a harin da rundunar sojin Najeriya ta kai ta sama, batun da rundunar sojin take shakku.

Shekarun Dorcas Maida Yakubu goma sha biyar lokacin da kungiyar Boko Haram ta sace ta, tare da kimanin ‘yan ajinsu mata dari uku, daga makarantarasu dake garin Chibok a arewa maso gabashin najeriya, cikin watan Aprilu shekara ta dubu biyu da goma sha hudu.

XS
SM
MD
LG