Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

IBB Ya Bayar Da Shawarar Mayar Da Majalisun Najeriya Su Zama Na Wucin Gadi


Tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Babangida
Tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Babangida

Tsohon Shugaban Nigeria Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bukaci a Maida Majalisun Dokokin kasar su zaman a wucin gadi domin rage makurdan kudaden da ake kashewa a kansu, dama wasu matsalolin da suka addabi Majalisun.

Janar Babangida, wanda ya zanta da manema labarai albarkacin cikarsa shekaru 75 yau Laraba, yace “A shekarar 1999, munyi kokarin mayar da Majalisu su zama na wucin gadi, domin rage yawan kudaden da ake kashewa akansu.”

Kalaman tsohon shugaban dai na zuwa ne a dai dai lokacin da Majalisar Wakilan Najeriya ta dauki zafi akan batun aringizon kasafin kudi. Daya daga cikin ‘yan Majalisar daga jihar Neja, Bala Faruk Bidda, ya tabbatar da cewa akwai tabargazar kudaden a Majalisar, ya kuma ce akwai shaida da take nuna barnar kudin da akayi.

Yan Najeriya dai na jiran ganin an dauki mataki akan lamarin Majalisar, kamar yadda Alhaji Lawali Shukura ke kira ga mahukunta na bangaren Shari’a da su tsaya su yi aikinsu tsakani da Allah, domin taimakawa gwamnati wajen farfado da halin da kasa ke ciki.

Saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari daga Minna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG