ABUJA, NIGERIA- A halin yanzu Najeriya ke kan gaba a jerin kasashen Afirka da ke da adadi mafi yawa na mutanen da suka bace, inda kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta ce akwai kimanin yara dubu 14,000 da suka yi batan dabo, adadin da ta ce baya cikin wanda a lokuta da yawa ake yin watsi da yaran.
Batun batan dabon mutane na daga cikin illolin yaki ko rikice-rikice mafi muni a kasashen duniya
A yayin bikin tunawa da ranar mutanen da suka bace ta duniya, shugaban kungiyar Red Cross a Najeriya Yann Bonzon, ya bayyana cewa adadin mutanen da suka bace a kasar na dada karuwa, lamarin da ke bukatar agajin gaggawa daga bangaren gwamnati.
‘’Ya ce a Najeriya kadai an samu adadi mafi yawa na mutanen da suka bace wanda kungiyar Red Cross ta tattaro adadin daga kasashen nahiyar Afirka. Tun lokacin tashin hankalin da aka fuskanta a shekarar 2009 a kasar, sama da mutane dubu 25,000 ne rahotanni suka nuna cewa sun bata, kazalika rahotannin sun nuna cewa an samu karin adadi na mutane kusan 2,000 da suka bata sakamokon rikice-rikicen da aka yi bayan watan Janairu na shekarar 2021 kuma ana cigaba da samun kari a adadin mutanen da ke bata.’’
Bonzon ya kara da cewa, adadin da aka tattaro ba ainijin yawan mutanen da suka bace ba ne a kasar, lamarin da ke nuni da akwai aiki nan gaba kan yawan wadanda ke ci gaba da bata musamman yara kanana.
Ya kuma kara da jan hankali kan cewa adadin da aka samu ya nuna musamman irin hadarin da ke tattare da yara idan aka kwatanta akan manya a Najeriya, kasar da har yanzu ake fama da tashe tashen hankula.’’
Hukumar kula da ayyukan jinkai a Najeriya ta bayyana cewa ba shakka adadin mutanen da suka bata ya zarta yadda rahoton kungiyar Red Cross ya bayyana, kamar yadda babban Sakataren hukumar Dakta Sani Gwarzo ya shaida.
Gwarzo ya kuma ce tuni Ministan Hukumar kula da ayyukan jinkan al’umma ta kasar Hajiya Sadiya Umar Faruk ta bada umarnin kirkiro da wani ofishi da zai kula da dukkannin lamuran da suka shafi mutanen da suka bata a kasar.
Mafi yawan lokuta dai iyalan wadanda suka bata kan kasance cikin kunci da tashin hankali sakamakon rashin sanin tabbas din halin da 'yan uwansu ke ciki.
Saurari rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim.