Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hanyar Samar Da Zaman Lafiya a Libya


Gen. Thomas Waldhauser
Gen. Thomas Waldhauser

Babban kwamandan sojojin Amurka dake Afirka ya fada wa Muryar Amurka cewa, hanyar kawai da za a iya samar da zaman lafiya a kasar Libya itace ta hado bangarorin dake fada da juna wuri guda.

Yace samun nasarar hakan ko yana bukatar kokarin sassa daban-daban, ciki ko har da kasar Rasha.

Janar Thomas Waldhauser, wanda ke shugabantar sojojin Amurka a Africa ya bayyana yadda ake ci gaba da samun tashe-tashen hankulan musammam na siyasa a kasar Libya sailin da yake wa zauren taron samar da tsaro bayani wanda akayi a Munich na kasar Jamani.

Yanzu haka dai kasar ta Libya ta rabu kashi-kashi, musali bangaren dake da goyon bayan gwamnatin hadin kan kasa na iko ne kurun da wani bangaren babban birnin kasar wato Tripoli, Yayin da bangaren dake adawa da gwamnati shi kuma yana iko da daya bangaren dama wasu birane.

Haka kuma wuraren dake yankin gabar tekun arewacin Africa na karkashin kulawar shugaban sojojin kasar ta Libya, Janar Khalifa Haftar, wanda kusan daukacin gabashin kasar na karkashin sa.

Waldhauser yace akwai bukatar ganin anyi wani abu game da wannan dinbin ikon Hafter dama yankin gabashin kasar ta Libya gaba dayan sa, domin nan ne matsalar siyasar kasar take.

Shi dai wannan yankin da babban sojabn kasar ke iko dashi nan ne inda ainihin inda arzikin man kasar yake.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG