Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Ta Sake Isra'ilawa 3 Yayin Da Isra'ila Ta Saki Fursinonin Falasdinawa 183


Israel Palestinians
Israel Palestinians

A ranar Asabar Hamas ta sake karin wasu mutane 3 ‘yan Isra’ila da take garkuwa da su kana itama Isra’ila ta maida martani da sakin frusinonin Falasdinawa 183 a musayar fursinonin ta bayan nan a matsayin wani bangare na Shirin tsagaita wuta.

Wannan ne karo na biyar da aka yi musaya tsakanin Hamas da Isra’ila tun fara Shirin tsagaita wuta a watan da ya gabata. Wannan dai na zuwa ne yayin da shugaban Amurka Donald Trump ke tallatar da shirinsa na mallakar Zirin Gaza.

Lafiyar mutanen 3 da aka yi garkuwa da su ya tada hankalin Isra’ilawan. Mutanen kuwa sun hada ne da Eli Sharabi mai shekaru 52 da Ohad Ben Ami mai shekaru 56, an sace dukkansu ne a Kibbutz Beeri, sai kuma Or Levy mai shekaru 34, wanda shi kuma aka sace daga wani bukin wake-wake na Nova a lokacin da Hamas ta kaddamar harin ranar 7 ga watan Oktoba 2023 a kan Isra’ila.

Mutane ukun suna cikin rama da raunin jiki, kana mayakan Hamas sun tilasta musu yin magana a wurin bukin mika su.

Wasu fursinoni da Isra’ila ta sake da yammacin ranar Asabar su kuma sun rame kana suna fama da raunin jiki. Red Cross ta ce ta kai mutum 7 zuwa asibitoci.

A cikin Falasdinawa 183 da aka saken, an yake wa 18 hukuncin rai-da-rai kana wasu 54 kuma suna fuskantar hukuncin zaman gidan yari na tsawon lokacin a kan abin da Isra’ila ta kira da samun hannun su acikin munanan hare haren da ake kaiwa Isra’ilan.

Wasu sun kwashe kimanin shekaru 20 a gidan yari. A garin Beitunia dake Yammacin Kogin Jordan, taron jama’a sun tarbi fursinonin a matsayin gwarzaye, suna daga tutoci kana suna rera taken goyon bayan Hamas.

Bugu da kari, a cikin wadanda aka saken, akwai Falasdinawa 111 daga Gaza da aka kama bayan harin da Hamas ta kai a kudancin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, harin da ya tada yaki a Gaza. An tsare su ba tare da shari’a ba, kuma Red Cross ta kaisu asibitin Turai a Khan Younis dake kudancin Gaza, inda wasu gungun mutane suka bazama a kan tituna suna murna.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG