Kungiyar Hamas a yau Alhamis ta bayyana shirinta na ci gaba da mutunta matsayar tsagaita wuta da ta cimma da Isra’ila yayin da masu shiga tsakani a rikicin suke kokarin ganin an ci gaba da bin wannan yarjejeniyar.
Kakakin kungiyar Abdel-Latif Al-Qanoua, ya ce Hamas ba ta da niyyar ganin rugujewar wannan yarjejeniya kuma a shirye take ta tabbatar da cewa ita ma Isra’ila ta mutunta matsayar.
“Netanyahu ya ce zai ci gaba da kai hare-hare a yankin Gaza idan har Hamas ba ta mutunta wannan yarjejeniya ba ta sakin wasu daga cikin mutanen da take garkuwa da su a ranar Asabar.”
Abdel-Latif ya soki “kalaman Firai Minista Netanyahu da na shugaban Amurka Donald Trump, yana mai cewa furucin na iya barazana ga shiri na tsagaita wuta da aka cimma.
A farkon makon nan Hamas ta zargi Isra’ila da keta matsayar ta hanyar ci gaba da kai hare-haren sama a yankin na Gaza hade da hana shigar da kayayyakin agaji.
Dandalin Mu Tattauna