A yayin wani taron manema labaran da suka kira a yammacin juma’a membobin kwamitin da ke bin diddigin abubuwan da suka biyo bayan turmitsitsin na ranar jifan shaidan suka tabbatar da cewa ya zuwa yanzu alhazai ‘yan nijer 78 ne suka rasu.
Shugaban kwamitin Ali Umaru ya kara da cewa yanzu haka ba a san inda alhazai 41 ‘yan nijer suka shiga ba, yayinda aka kyasta cewa mutane 34 da suka ji rauni. Ya bayyana cewa, daga cikin mutane da suka rasu, arba’in da hudu ne kawai aka yiwa takardun rajistar mamata.
Kwamitin ya karyata jita- jitar da ake yayatawa cewa, cikin rami guda aka bunne gawawakin mutanen da suka rasu a turereniyar ta mina. Ya bayyana cewa, an yiwa kowacce gawa sutura yadda ya kamata.
Shugaban kwamitin bin diddigi halin da alhazan nijer suka shiga a yayin wannan iftila’i ya bukaci jama’a su kara hakuri yayinda ake neman karin bayanai kan sauran alhazan da har yanzu ba a tabbatar da halin da suke ciki ba. Bisa ga cewarsa hukumomin Saudiya na ci gaba da tantance ragowar gawarwakin alhazai ta hanyar binciken zanen yatsu domin tantance sunayensu da kasashen da suka fito.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Sule Mumuni Barma