Mahukuntar kasar Yemen sun ce sojoji masu biyayya ga yan tawayen Shia na Houthi sun samu nasarar karbe babban filin jirgin saman birnin Arden, yan awoyi kadan bayan da shugaban kasar ya bar gidan sa dake babban birnin kasar.
Samun nasarar karbe wannan filin jirgin ya kawo dakatar da harkoki a tashar jirgin tun jiya Laraba domin ko yan shia na Houthi din sun samu goyon bayan wasu sojoji ne da suka mara musu baya wanda har yasa suka yi nasarar shiga birnin kuma suka yi nasara.
Tun farko a ranar Larabar data wuce jirgin yakin Yemen, wanda yan tawayen na ke sarrafawa, su da magoya bayan su, suna kaiwa fadar shugaban kasar hari ne a birnin na Arden.
Sai dai jami’angwamnatin kasar sunce shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi ya tsira da ransa kuma yana wani wurin da ba a bayyana ba.
Daya daga cikin hadiman shugaban kasan Mohammed Meran ya shaidawa kanfanin dillacin labarai na Reuters cewa shugaban yana nan lafiya kuma sojojin kasar suna karban umurni daga gare shi na ganin cewa yan tawayen basu samu nasarar shiga cikin birnin kasar ba.
Sai dai an samu rahotanni masu karo da juna game da inda shugaban kasan yake, domin jami’an fadar White House sun ce ba zasu gasganta rahoton dake cewa shugaban kasar ya bar kasar ba.