Al’umah da dama kanyi amfani da wannan watan na Azumi wajen aiwatar da ayyuka masu dunbin lada, amma bayan watan kuwa sai ka ga akasin haka. To wai me ke kawo hakan? A ta bakin wasu malamai suna ganin cewar mafi akasarin mutane sunayi wadannan ibadun ne badan Allah, ba sukanyi su ne don agani a yabamusu, shiyasa za’aga cewar irin wannan ibadar bata daurewa.
Mafi alfanu shine mutane suji tsoron Allah, kuma sukasance masu yin Ibadan don Allah, badan wani yaganiba, ta haka shine kawai zasu iya cigaba da waddannan ibadun koda bayan azumi, kana su kuma sani wannan wata ne da ake da bukatar mutun ya kokarta wajen chanza halayensa, da mu’amalarsa da jama’a, da dai duk wasu abubuwa da zasu kusantar dashi zuga Allah.
Wasu bayin Allah, da suka bayyanar da nasu fahimtar da watan azumi, sunce gaskiya abune mai matukar wahala ace sunyi wasu ayyuka na ibada a watan daba na azumi ba, amma muddun akace watan azumi ya tsaya to sukanyi kokari wajen aikata ayyuka na alkhairi fiye da kima, suna kuma fatar Allah, ya basu ikon cigaba da aiwatar da irin wadannan ibadun da ma wasu acikin sauran watanni bayan ramadana.