Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Sababbin Jam'iyyu Na Shirin Bada Mamaki a Zaben Da Ake a Spain


Shugaban Kasar Spain
Shugaban Kasar Spain

A yau Lahadi masu kada kuri’a a kasar Spain sun nufi rumfunan zaben da masu tsokaci ke ganin zai iya zama zaben ‘yan majalisar dokoki mafi tarihi a kasar.

Sababbin jam’iyyun kasar guda biyu ne ake ganin zasu iya bawa tsoffin jam’iyyun kasar mamaki a zaben.

Musamman jam’iyyar ‘yan gurguzu da kuma ta Firaministan kasar Mariano Rajoy masu ra’ayin ‘yan mazan jiya. Sauran kuri’un ragowar jam’iyyu guda 3 kuma ana ganin kashe ta yiwu sai dai ayi raba daidai.

Wanda hakan zai bawa sabbin jam’iyun dama taka rawar ganin. Wannna sauyin yanayin siyasar zai girgiza salon siyasar kasar ta Spain inda masu kada kuri’ar ke tururuwa kamar da kaso 80 ba kamar a bay aba da basu wuce kaso 69 ba a shekarar 2011.

Tattalin arzikin Spaniya dai ana sa ran zai kara dagawa da kaso 3 a bana, wanda hakan zai sa wasu kasashen Turan jin da ma su ne za su yi wannan nasarar, sai dai har yanzu kasar na fama da matsalar rashin aikin yi da rashin daidaita tsakani.

XS
SM
MD
LG