Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nigeria Za Ta Shawo Kan Matsalar Wutar Lantarki


 Babatunde Fashola, ministan makamashi, ayyuka da gidaje na Nigeria
Babatunde Fashola, ministan makamashi, ayyuka da gidaje na Nigeria

A taron masu ruwa da tsaki da aka yi a Minna , jihar Niger akan matsalolin wutar lantarki a Nigeria, ministan makamashi da ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola da kwamishanan ayyuka na jihar Niger sun amince cewa rashin mitoci da rashin kayan zamani na raba wutar ke kwao cikas

Gwamnatin Nigeria ta ce tana ci gaba da nemo hanyoyn shawo kan matsalar da ta addabi wutar lantarki a kasar.

A wani babban taron masu ruwa da tsaki a harkokin wutar lantarki, Ministan Makamashi da Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola ya ce taron na Minna zai maida hankali ne akan matsalolin da suke kawo cikas a harkokin wutar lantarki.

Ministan y ace ana fuskantar matasloli biyu ne, samun mitoci ga masu anfani da ita da kuma raba wutar. Ya yi imanin cewa a taron zasu ji bahasinsu daga bakin masu ruwa da tsaki a kan harkokin wutar lantarkin.

Kwamishanan ayyuka na jihar Niger Alhaji Ibrahim Balarabe wanda ya halarci taron ya ce taron yana da anfani matuka a daidai wannan lokacin. Alhaji Balarabe y ace akwai wuta amma masu raba ta suna da matsalar ingantattun kayan aiki irin na zamani. Kalubalen dake fuskantarsu ke nan har sai sun samu kayan aikin da suka dace.

A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG