Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin kasar Somaliya tayi yi tir da musanta fama da yunwa a kasar da kungiyar mayaka tayi


Somaliyawan da yunwa ta tilastawa gudun hijira suna jira a raba masu abinci a sansani
Somaliyawan da yunwa ta tilastawa gudun hijira suna jira a raba masu abinci a sansani

Gwamnatin kasar Somali da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya ta yi allah wadai da shawarar da kungiyar mayakan da ake alakantawa da kungiyar al-Qaida ta yanke ta hana ma’aikatan agaji shiga kasar duk da matsananciyar yunwa da ake fama da ita.

Gwamnatin kasar Somali da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya ta yi allah wadai da shawarar da kungiyar mayakan da ake alakantawa da kungiyar al-Qaida ta yanke ta hana ma’aikatan agaji shiga kasar duk da matsananciyar yunwa da ake fama da ita. A cikin sanarwar da ya bayar yau asabar, PM Abdiweli Mohammed ali ya kuma argi kungiyar al-Shabab da hana mutane ficewa daga yankin dake karkashin ikonta domin su nemi abinci. Ya yi kira ga al’ummar kasa da kasa su tallafa da abinci da kuma marawa gwamnatin baya a yunkurinta na murkushe mayakan. Kungiyar Tarayyar Afrika ta tura dakarun kiyaye zaman lafiya dubu takwas domin marawa gwamnatin kasar Somaliya baya wajen shawo kan hare haren da kungiyar al-shabab ke kaiwa. A cikin wannan makon Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da fama da mummunar yunwa a yankin Bakool dake kudancin Somaliya da kuma Shabelle dake kurya, cibiyar ta kuma ce kimanin rabin mutanen kasar Somaliya suna bukatar agajin gaggawa.

Jiya jumma’a cibiyar lafiya ta duniya tace yankunan Somaliya biyar kuma suna dab da tsunduma cikin bala’in yunwa. Sai dai kungiyar al-Shabab tace farfaganda ce kawai Majalisar Dinkin Duniya take yi da batun bala’in yunuwar. Kakakin kungiyar al-Shabab Sheikh Ali Mohamoud ya zargi Majalisar Dinkin Duniya da kara gishiri a bala’in sabili da dalilan siyasa. Ya ce kungiyar zata kyale kungiyoyin agajin dake aiki a halinyanzu a yankin da take iko ne kawai su kai dauki, amma ba kungiyoyin da ta haramtawa ba. Sai dai bai ambaci sunayen kungiyoyin ba. Jiya jumma’a kasar Canada tace zata kara tallafin ayyukan jinkan da take badawa a gabashin Afrika da dala miliyan hamsin yayinda kasar Venezuela kuma tayi alkawarin bada karin dala miliyan biyar. Babu tabbacin ko kasashen Canada da Venezuela na daga cikin cibiyoyin agajin da kungiyar al-Shabab ta haramtawa gudanar da ayyukan jinkai. A halin da ake ciki kuma cibiyar tsugunar da ‘yan gudun hijira ta MDD ta ce adadin ‘yan kasar Somaliya dake mutuwa a sansanin ‘yan gudun hijira dake kasar Habasha da Kenya sakamakon karancin abinci yana karuwa yayinda Samaliyawa ke ci gaba da kauracewa kasar.

XS
SM
MD
LG