Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Hukunta Duk Wanda Aka Samu Da Hannu A Dukan Dan Bilki - Gwamnatin Kaduna


Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani

“Gwamnatin jihar Kaduna tana nesanta kanta daga wannan mummunan aiki. Wannan ba halinmu ba ne. Irin wannan aiki na rashin imani ba shi da hurumi a cikin al’uma ta gari."

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya sa a gudanar da bincike kan wani bidiyo da ya nuna wasu jami’an tsaro suna zane wani mutum mai suna Dan Bilki Commander bayan da suka zarge shi da laifin sukar gwamnan.

Bidiyon, wanda ya karade shafukan sada zumunta a ranar Alhamis ya nuna Dan Bilki sanye da ankwa wasu mutane da ake zargin jami’an tsaro ne suna mai tambaya kan dalilin da ya sa yake zagin gwamnan jihar Kaduna.

Daga baya, an ga mutanen wadanda ba a nuna fuskokinsu ba suna cauda masa bulala yayin da shi kuma yake ce musu su bar dukan shi domin yana da ciwon suga da hawan jini.

Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin jihar ta Kaduna ta nesanta kanta da wannan al’amari.

“An jawo hankalin gwamnatin jihar Kaduna kan wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, inda aka nuna wasu mutane da ba a san ko su waye ba, suna zane wani Dan Bilki Commander. A cikin bidiyon ana zargin gwamnatin jihar Kaduna.”

“Gwamnatin jihar Kaduna tana mai nesanta kanta daga wannan mummunan aiki. Wannan ba halinmu ba ne. Irin wannan aiki na rashin imani ba shi da hurumi a cikin al’uma ta gari.

“Gwamnan jihar Kaduna, mutum ne da ya jima yana fafutuka kan kare hakkin bil Adama da ‘yancin walwala.” Wata sanarwa dauke da sa hannun Sakataren yada labaran jihar Muhammad Lawal Shehu ta ce.

Sanarwar ta kara da cewa, a dalilin haka, Gwamna Uba Sani ya sa a kaddamar da cikakken bincike kan wannan al’amari.

“Gwamna ya kuduri aniyyar ganin an zakulo gaskiyar al’amarin, kuma duk wanda aka samu da hannu zai fuskanci fushin hukuma.” In ji Shehu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG