Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kaduna Ta Gindaya Sharuddan Jinyar El-Zakzaky


Sheik El-Zakzaky
Sheik El-Zakzaky

A karshe dai gwamnatin jahar Kaduna ta bayyana aniyar daukaka kara kan hukuncin da babbar kotun jahar ta yanke game da baiwa jagoran mabiya Shi'a a Najeriya damar zuwa Indiya domin duba lafiyar shi da ta mai-dakin shi.

Gwamnatin ta ce duk da yake dai ba muzgunawa Mal. El-zazzaky ta ke son yi ba, akwai bukatar shimfida ka'idoji kafin wadanda ake karar su fice zuwa Indiya.

Gwamnatin ta gindaya ka’idoji bakwai da tace tilas a cika kafin barin El-Zakzaky da mai dakinsa su tafi jinya. Na farko gwamnatin tace, tana so gwamnatin tarayyar Najeriya ta binciko ko asibitin ya yi shirin karbar jinyarsa da kuma tabbatar an kiyaye ka’idojin jinyar. Banda haka kuma sai masu jinyar sun dauki alkawarin cewa, zasu dawo Najeriya idan aka sallame su daga asibiti, kuma sune zasu dauki nauyin dukan dawainiyar tafiyar da kuma jinyarsu.

Wasu daga cikin sharuddan da gwamnatin jahar Kaduna ke son a shimfada wa sheikh El-zazzaky da mai-dakin shi kafin fita Indiya neman lafiyar dai sun hada da kawo babban sarki Mai daraja ta daya, da kuma sanannen mutum da za su tsaya musu Ana kuma bukata Mal. El-zazzaky da mai-dakin da lauyoyin su su dauki rantsuwa cewa da sun sami lafiya za su dawo Nigeria, sannan kuma za a hada su da jami'an tsaro na gwamnatin tarayya su zauna da su har zuwa ranar da za su dawo gida Najeriya.

Har wa yau, gwamnatin jihar Kaduna ta bukaci ofishin jakadancin Najeriya a kasar India ta sa ido sosai ta kuma tantance duk wanda ya nemi ganin wadanda ake tuhuman, banda haka kuma ya kasance babu wanda zai iya ganinsu sai da izinin ofishin jakadancin Najeriya.

Saurari cikakken rahoton Isa Lawal Ikara.

Kaduna zata daukaka kara kan El-Zakzaky-3:48"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG