Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Naija Tana Kokarin Hana Yaduwar Shan Inna


Yaki da Cutar Shan Inna a Najeriya
Yaki da Cutar Shan Inna a Najeriya

Gwamnan Jihar Niger, Dr Mu’azu Babangida Aliyu, ya umurci shugabannin kananan hukumomin da suke kan iyaka da wadansu jihojin tarayya su karfafa yin allurar rigakafi domin kiyaye yaduwar kwayar cutar shan inna daga jiha zuwa jiha.

Gwamnan Jihar Niger, Dr Mu’azu Babangida Aliyu, ya umurci shugabannin kananan hukumomin da suke kan iyaka da wadansu jihojin tarayya su karfafa yin allurar rigakafi domin kiyaye yaduwar kwayar cutar shan inna daga jiha zuwa jiha.

Aliyu, wanda bayyana cewa jihar ta zama babu cutar inna, yace, dole a karfafa yin allurar rigakafin domin kiyaye yaduwa daga wadansu jihohin su damin jihar da bata da cutar inna.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen wani taron yaki da cutar shan inna karo na bakwai wanda kwamishinar ma;aikatar mata Hajiya Hassana Adamu ta wakilce shi. Gwamna Babangida Aliyu ya bayyana damuwa ganin an sake samun bullar kwayar cutara shan inna a wannan shakara a wadansu jihohin arewaci na tsakiya.
Yace ana bukatar kara kokari idan ana so ci gaban da aka samu ta dore a kuma iya kawar da cutar da kuma yanayin da yake kara yaduwarta a jihohin da ake fama da sake bullar cutar.

Ya kuma yi kira ga dukan sassan kananan hukumomin dake makwabtaka da jihohi masu fama da wannan cutar, cewa dole suyi kokari su tabbatar an yiwa dukan yara dake kasa da shekara biyar rigakafin domin kiyaye yaduwar cutar. Ya bayyana cewa ci gaba da samun bullar cutar shan inna abin damuwa ne ga kasa baki daya, bisa ga cewarshi, an shafe sama da shekara daya ba a sami wani yaro da cutar ba a jihar Naija. Duk da haka yace gwamnati zata ci gaba da kara kokari domin ganin an cimma nasara.
Dalili ke nan inji shi da yasa jihar ta sami gudummuwa da yabo daga gidauniyar Bill da Melinda gate domin kokarin da take yi a fannin rigakafin.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG