Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Gombe ta Tallafawa Masu Sufuri da Kananan Motoci 500


Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo
Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo

A yunkurinta na neman taimakwa jama'a da samun ababen hawa a saukake gwamnatin jihar Gombe ta tallafawa masu sufuri da kananan motoci dari biyar

A kokarin ganin an saukakawa al'ummomin jihar Gombe gwamnatin jihar ta samarma masu aikin sufuri kananan motoci dari biyar.

Matsalar samun abun hawa a kan kari musamman a cikin garin Gombe abu ne da ya damu kowa musamman wadanda basu da nasu ababen hawan. Mutane musamman mata da yara sukan kwashi sa'o'i da yawa kafin su samu motocin da zasu kaisu inda zasu.

Sabili da rage wannan matsalar gwamnatin jihar ta samarda kananan motoci da za'a yi anfani dasu a jihar musamman cikin babban birnin dake zama fadar gwamnatin. Gwamnatin tana cigaba da raba motocin ga kungiyoyi kamar yadda kwamishanan kudi na jihar Alhaji Hassan Muhammed ya bayyana. Yace gwamnan ne ya bayar da umurni a saki motocin ga kungiyoyi a kokarin inganta sufuri da kuma habaka tattalin arzikin jihar. Shirin ya baiwa wadanda aka ba motocin zarafin biyan kudin motocin a hankali har su gama biya kana motocin su zama mallakarsu.

Manyan kungiyoyin sufuri a jihar su ne suka fara cin gajiyar shirin a karon farko. A wannan karon kananan kungiyoyin sufuri ake rabama motocin. Su dai motocin an tanadasu ne domin a yi aikin sufuri dasu cikin gari. Kwamishanan kudin ya kara da cewa laifi ne mutum ya dauki motar da aka bashi ya kaita wani garin da baya cikin jihar yana anfani da ita.

Ga Sa'adatu Fawu Mohammed da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG