Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Borno Ta Hana Zirga Zirga A Wadansu Hanyoyi


Operation Lafiya Dole
Operation Lafiya Dole

A jiya ne gwamnatin jihar Borno ta fitar da wata sanarwar inda ta haramta zirga zirga a wadansu hanyoyin dake fadin jihar.

Gwamnatin tace sanarwar zata kama aiki ne nan take daga jiya litinin har zuwa hudu ga watan Fabrairu. Sanarwar dai tana dauke da sa hannun kwamishinan ma'aikatar watsa labarai da al’adun cikin gida na jihar Borno Dr Mohammed Bulama da aka aikawa kafofin yada labarai a yammacin jiya.

Sanarwar tace an haramta zirga zirgar dukan motocin hawa ne na fararen hula dakan tashi daga garin Maiduguri zuwa Kwandiga, da Bama zuwa Banki, da kuma daga Banki zuwa garin Bama, sai kuma daga garin Bama har zuwa Goza wanda har zai dangana da birnin Maiduguri.

Har ila yau mabiya wata hanya da ake kira Mulai da ta tashi daga garin Maiduguri da zai gangara har zuwa garin Dambuwa da Goza, nan ma an haramtawa al’umma bin wannan hanyar, har sai rundunar tsaro ta kammala ayyukan da take yin a kakkabe gyauron ‘yan kungiyar Boko Haram.

Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Bi’u daga Maiduguri.

An rufe wadansu hanyoyi a jihar Borno-1:48"
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:48 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG