Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Ghana Ta Karawa Ma’aikata Albashi Da Kashi 30 Cikin Dari


Taron Karin Albashi Tsakanin Gwamnatin Ghana Da Kungiyar Kwadago 1
Taron Karin Albashi Tsakanin Gwamnatin Ghana Da Kungiyar Kwadago 1

Gwamnatin kasar Ghana ta kara wa ma'aikata albashi bayan rashin samun daidaito a yarjejeniyar kara albashi da kashi 60 cikin 100 tsakanin Kungiyar Kwadago da Gwamnatin.

Daga baya dai gwamnatin Ghana ta fitar da wata sanarwa da ta nuna cewa ta kara albashin dukkan ma'aikatan gwamnati da kashi 30 cikin 100 kuma zai fara aiki daga ranar daya ga watan nan na Janairun shekara ta 2023.

Hakan ya biyo bayan wata ganawa da kungiyar kwadago ta shirya a jiya Alhamis, bayan tattaunawa goma da aka dinga yi tsakanin bangarorin biyun, amma ba'a yi nasara ba.

Kungiyar kwadagon dai da farkon tattaunawar ta bukaci karin albashi kashi 60 cikin 100, yayin da kudurin farko na gwamnati shine kashi 18 cikin 100, bayan jayayya da aka tabka kungiyar ta yanke shawarar rage kashi 2 cikin 100 a cikin kashi 60 cikin 100 wato ya zama kashi 58 cikin 100.

Taron Karin Albashi Tsakanin Gwamnatin Ghana Da Kungiyar Kwadago 2
Taron Karin Albashi Tsakanin Gwamnatin Ghana Da Kungiyar Kwadago 2

Ministan kudin Ghana Ken Ofori-Atta a taron ya lura cewa karin zai kawo cikas ga harkokin kudin kasar.

Ya ce "kamar yadda na ambata hakan zai yi tasiri a kasafin kudi, amma muna da yakinin za mu inganta samar da ayyukan yi da kuma jajircewar da muka yi wa junanmu na ganin an samu zaman lafiya a kasar nan yayin da muke duba kudaden fansho da kwadago."

Wasu ‘yan kasar Ghana sun nuna rashin gamsuwarsu game da karin albashin kashi 30 cikin 100, inda suke cewa wannan karin ba zai yi musu komai ba duba da irin yadda rayuwa ta kara yin tsada sosai.

Saurari cikakken rahoton Hawa Abdulkarim:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00

Zaben 2023

Kudurin wasu 'yan Najeriya na sabuwar shekara a fannin lafiya, da wasu sauye-sauyen da suke fatan yi don samun nasara a rayuwarsu
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p

No media source currently available

0:00 5:16 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG