Shugaban kasar China Xi Jinping ya ayyana “Yakin al'umma” akan barkewar cutar Coronovirus, yayin da ake kara samu karuwar adadin wadanda suke mutuwa a kullum.
Kamfanin dillancin labaran kasar China na Xinhua ya ambaci ta bakin shugaba Xi yana cewa.“Gaba daya kasar mu ta dauki matakai tare da dukkan karfinta na tsaurara matakan kariya da kuma matakan magance cutar, fara yakin al'umma na hana yaduwa da magance cutar".
Jami’ai a Lardi Hubei, inda cutar ta barke, sun bada rahoton mutuwar wasu karin mutane 69 a yau juma’a da safe, da ya kawo adadin wadanda suka mutu da kwayar cutar zuwa sama da mutane 630. Sannan an bada rahoton mutane 2,500 sabbi da suka kamu da cutar, da ya kara adadin sama da mutane dubu 30,000 da suka kamu da cutar.
Yanzu haka akwai kusan mutane 150 da aka tabbatar sun kamu da cutar a sauran kasashe, ciki har da mutuwar mutun daya a kasar Philippines, wanda shine na farko a wajan kasar China, kan da mutuwar mutun daya a Yankin Hong Kong.
Facebook Forum