A nan Amurka kuma…Gwamnatin shugaba Donald Trump tace tana niyyar ta rage yawan mutanen dake shigowa cikin Amurka da sunan ‘yan gudun hijira – kuma ragi mai yawan gaske, duk kuwa da rokon da kungiyoyin kare hakkokin Bil Adama ke yi na cewa, maimakon a rage, kwanda ma a kara yawan wadanda zasu iya shigowar.
A cikin wani rahoton da ta aikawa Majalisar Dokokin Amurka din a jiya ne, fadar shugaban Amurka ta White House take cewa yawan mutane, ‘yan gudun hijiran da gwamnatin zata bari su shigo a cikin shekarar da za’a shiga ba zasu wuce 45,000 ba, wanda kuma wannan itace jimilla mafi kankanta a cikin shekaru 35 da suka gabata.
Kafin ya sauka daga karagar mulki, tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya bada shawarar ribanya yawan ‘yan gudun hijiran da za’a bari su shigo Amurka, inda ya nemi a bude hanya ga akalla masu yawan 110,000.
A zaman mulkin shekaru takwas da yayi, ‘yan gudun hijira kusan 885,000 Obama ya budewa hanyar shigowa Amurka.
Facebook Forum