WASHINGTON DC, —
Wani bincike da aka gudanar, ya bayyanar da kasashe ashirin
da biyar 25, da su kafi kudi a duniya, da yadda kasashen suke
samun kudin su. Ga jeri kasashen.
Kasar farko itace kasar “Qatar” wadda take cikin daular
kasashen larabawa. Kasar dai nada karfin tattalin arziki dake
bayyanar da kwatankwacin kudin da kowane dan kasar yake samu a
shekara.
Kasar dai da keda yawan mutane 2,172,065. Mutane
kansamu albashi daya kai dallar Amurka $139,760 dai-dai da
naira 27,952,000 a shekara. Kana mutane kanyi rayuwa har na
tsawon shekaru 79, kamun mutuwa.
Baki daya a shekarar 2016 an kiyasta kasar na da karfin arziki
GDP da ya kai dallar Amurka $211.8 Billiyan. Dai-dai da naira
tiriliyan 42,360,000,000,000 Karfin kudin su daga albarka mai
ne wanda suke na 9, a duniya da sukafi kowace kasa yawan wajen
ajiye mai.
Sai kasa ta biyu mai karfin arziki a duniya, itace kasar
“Macao Sar, China” Kasar dai nada karfin tattalin arziki dake
bayyanar da kwatankwacin kudin da kowane dan kasar yake samu a
shekara.
A kasar dai da keda yawan mutane 577,914. Mutane
kan samu albashi daya kai dallar Amurka $118,110 dai-dai da
naira 23,622,000 a shekara. Kana mutane kanyi rayuwa har na
tsawon shekaru 80, kamun mutuwa.
Baki daya a shekarar 2016 an kiyasta kasar na da karfin arziki GDP da ya kai dallar Amurka $55.5 Billiyan dai-dai da naira tirilliyan 11,100,000,000,000. Karfin kudin su daga ca-ca ne, inda ta zama babban birnin ca-ca a yankin kasashen Asia.
Kasa ta 3, da tafi kudi a duniya kuwa itace kasar “Kuwai” Kasar dai nada karfin tattalin arziki dake bayyanar da kwatankwacin kudin da kowane dan kasar yake samu a shekara. A kasar dai da keda yawan mutane 3,753,121. Mutane kan samu albashi da ya kai dallar Amurka $82,210 dai-dai da naira 16,442,000 a shekara. Kana mutane kanyi rayuwa har na tsawon shekaru 75, kamun mutuwa .Baki daya a shekarar 2016 an kiyasta kasar na da karfin arziki GDP da ya kai dallar Amurka $175.8 Billiyan. Dai-dai da naira tirilliyan 35,160,000,000,000 Kamar kasashen duniya goma, kasar Kuwai, karfin kudin su daga arzikin man fetur ne.