Da yake jawabi bayan hawan sallah a jihar Katsina, gwamna Aminu Bello Masari, ya gabatar da sakon shugaban ‘kasa inda yace shugaban yace a isar da godiyarsa ga mutanen Katsina kan addu’o’in da suke yi masa, ganin yadda Allah ya amsa addu’ar mutanen Najeriya.
Tun da farko da yayi nasa jawabin mai martaba sarkin Katsina Alhaji Dakta Abdulmuminu Kabir Usman, ya yabawa gwamnatin jihar Katsina saboda maido da tsaffin malamai da ta yi bakin aiki. Inda ya bayyana muhimmancin matakin ilimin firamare mai zama ginshiki a rayuwa.
Shima anasa jawabin gwamna Masari ya nanata muhimmancin ilimin fimare, ya kuma yi kira ga al’umma da tsaffin malamai da sauran wadanda ke da ilimin koyarwa da su taimaka don ilimantar da yara a duk fadin jihar.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum