Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Babbar Sallah A Yola Jihar Adamawa cikin Matakan Tsaro


Lamidon Adamawa, Sarakuna da Majalisarsa a filin idi lokacin babbar sallah yau a Yola
Lamidon Adamawa, Sarakuna da Majalisarsa a filin idi lokacin babbar sallah yau a Yola

A Yola babban birnin jihar Adamawa Lamidon Adamawa da sarakuna da majalisarsa da gwamnan jihar suka halarci filin idin birnin inda suka gudanar da sallah.

Yayin da al’umman Musulmi a fadin duniya ke gudanar da bikin Sallar layya,rahotanni daga jihohin Adamawa da Taraba na cewa an gudanar da sallar cikin koshin lafiya,yayin da aka dakatar da gaisuwar sallar da aka saba kowace shekara

Tun da sanyin safiya ne jama’a suka soma tururuwa domin gudanar da Sallar layyan cikin matakan tsaro da tsanaki,inda limamai suka gabatar da hudubobi kan muhimmancin laihar,taimako da kuma zaman lafiya dake zama tubalin cigaba.

Lamidon Adamawa,Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa,tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ,Bamanga Tukur da wasu manyan 'yan siyasan Najeriya na cikin wadanda suka halarci sallar a Yola da Khadi Ahmadu Bobboi ya jagoranta.

A sakonsa jim kadan da idar da Sallar,gwamnan jihar Adamawa Sanata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla ya bukaci 'yan Najeriya da su cigaba da yin addu’ar samun zaman lafiya .

Duk dai da matsin tattalin arzikin da 'yan kasar ke fama da shi, jama’a da dama sun sami damar yin layya,yayin da wasu ke cewa "Allah San barka".

Suma dai yara ba’a barsu a baya ba wajen bayyana farin cikinsu kamar.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG