Gwamnatin Tarayya dai ta kafa kwamitin da ke zagayawa jihohi domin tattara bayanai akan yadda za a gina Burtalin da zai taimakawa Fulani domin kawo karshen hatsaniyar da ake samu tsakanin Fulani Makiyaya da Manoma.
Jagoran wannan kwamiti zuwa jihar Kaduna Alhaji Mohammadu Salihu Ahmed, wanda yake darakta ne a ma’aikatar Noma ta Tarayyar Najeriya. Yace rashin Burtalin da Fulani ke kiwo na daya daga cikin makasudin fututtunun da ake samu kasa, hakan yasa gwamnatin Tarayya ta amince da a sake gina Burtalin a jihohin da ake bukata.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah na Najeriya, Alhaji Mohammadu kirwa, yana daga cikin ‘ya ‘yan wannan kwamiti da aka kafa, yace kwamitin zai fara shiga cikin daji yana tara Fulani domin jin shawararsu kan wannan batu.
Kwamitin dai na tattara bayanai ne wajen ganin an samu matsaya akan samar da Burtalin da Fulani zasu ringa kiwo ba tare da sun ci gaba da yawon da za a rinka rikici tsakaninsu da manoma ba.
Saurari cikakken rahotan Isah Lawal daga jihar Kaduna.