Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Gombe Ya Sassauta Dokar Ta Baci da Ya Kafa


Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo
Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo

Biyo bayan harin da aka kai a jihar Gombe, gwamnan ya kakabawa wurin dokar ta baci na ba fita dare da rana lamarin da ya zo ma wadanda abun ya shafa bazata.

Umar Alkali mai taimakawa gwamnan jihar Gombe ta fuskar labarai ya bayyana wa jama'a cewa gwamnan ya yiwa dokar sassauci.

Gwamnan jihar Hassan Dankwambo ya sassauta dokar daga karfe takwas na yamma zuwa karfe shida na safiya, wato babu fita daga wannan lokacin. Mutane na iya yin zirga-zirgansu daga karfe shida na safe zuwa takwas na yamma.

An kira mutane su bada hadin kai da goyon baya musamman ga jami'an tsaro da masu ayyuka na musamman irin su 'yan jarida da 'yan kwana-kwana, ayyukan kiwon lafiya da makamancinsu.

Mutane sun furta albarkacin bakinsu dangane da sassaucin da gwamnan yayi. Jama'a sun yi murna da sassaucin domin mutane zasu sami walwala kuma za'a fita a nemi abinci kasancewa dokar ta zo masu bazata ne.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG