Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Borno, shima yayi Tsoakci Akan Majigin VOA Akan Boko Haram


Gwamnan Borno Kashim Shettima
Gwamnan Borno Kashim Shettima

Cikin kwanaki biyu da aka yi a jihar Borno ana nuna majigin Muryar Amurka akan Boko Haram mai taken “Tattaki daga Muguwar Akida” gwamnan Borno da wasu cikin mukarrabansa sun kalla kuma sun yaba da aikin da aka yi

Jihar Borno it ace jihar da ta fi kowace jiha fuskantar matsalar rikicin Boko Haram wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubun dubatan mutane tare da raba miliyoyin jama’a da gidajensu.

Gwamnan Borno Kashim Shettima na cikin mayan mutanen da suka kalli majigin. Muryar Amurka ta tambayeshi abun da zai iya cewa akan majigin.

Yace Muryar Amurka tayi aiki nagari. Yace ko shakka babu zai ilimantar da mutane, ya nuna cewa akidar Boko Haram bakar akida ce. A cewarsa majigin zai ceto matasa da yawa daga fadawa cikin wannan muguwar akida.

Shi kuma Mallam Muhammad Jibrin cewa yayi majigin ya nuna masa abun da bai taba tsammanin zai gani ba. Ya ga aikin rashin Imani da ‘yan Boko Haram suka yi. Yace abun da suka yi abun takaici ne.

Shi ko Umaru Muhammad y ace majigin ya koya masu darussa da dama. Y ace duk wadanda basu gani bas u nemi, ya kamata su gani.

Sai dai Umaru Umar Kassim y ace tunda abun a Borno ya faru kamata yayi kafofin yada labaran Borno ne suka yi majigin amma sai gashi Muryar Amurka ce tayi. Saboda haka ya y aba wa VOA.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG