Da yake hira da 'yan jarida a Bauchi, gwamna Yuguda, yace huduba da kuma nasihar iyayen kasa, sune suka sanya shi ya canja ra'ayinsa. Yace wasu iyayen kasa da yawa sun ba shi shawara, ganin cewa maganar babba, maganar basira ce, suka ce masa da lallai ya hakura ya ci gaba da halartar wannan taro.
Yace da ma ba wai ya janye Jihar Bauchi ne daga cikin taron ba, shi ne ya janye kansa a kan ba zai rika halartar taron ba. Yace ya ji zafin cewa an yi taro na gwamnonin arewa, an yi yarjejeniya an kuma dauki alkawari, amma da aka je wajen taro sai aka yi wani abu sabanin hakan.
Sai dai kuma, gwamna Yuguda yace shi kam har yanzu yana kan bakarsa ta cewa gwamna Jonah Jang na Jihar Filato, shi ne shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, tunda gwamnoni 19 daga cikin 36 sun yi alkawarin zabensa tun farko.
A wajen zaben na ainihi da aka gudanar dai, gwamnoni da dama daga yankin arewacin Najeriya ba su zabi shi Jang ba, wanda ake ganin dan lelen fadar shugaban kasa ne. Gwamna Rotimi Amaechi na Jihar Rivers, shi ne a karshe ya lashe zaben da kuri'u 19, yayin da Jang ya samu 16.
Ga cikakken bayanin Malam Isa Yuguda daga bakinswa.