Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guterres Ya Nemi a Gudanar Da Bincike Kan Rikicin Falasdinu Da Isra'ila


Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres yayin wani taorn kwamitin sulhu na majalisar kan rikicin Syria
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres yayin wani taorn kwamitin sulhu na majalisar kan rikicin Syria

Bayan rayukan Falasdinawa 15 da suka salwanta a rikicin da ake yi a kan iyakar Isra'ila da Gaza, babban Sakatare na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya nemi da aka gudanar da bincike.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa, kan mummunar arangamar da ta auku akan iyakar Isra’ila da yankin Gaza a jiya Juma’a.

Arangamar ta yi sanadin mutuwar Falasdinawa 15, kana wasu 1,400 suka jikkata, ciki har da mutane 750 da suka ji raunuka sanadiyar harbin bindiga.

A jiya Juma’a kwamitin Sulhu na Majalisar ya gudanar da wani taron gaggawa, domin tattauna takaddamar da ta kaure a yankin na Gaza.

Amma ba a cimma wata matsaya ba.

Jakadan Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya, Danny Danon, ya ce an gudanar da taron gaggawan, duk da cewa Amurka da Isra’ila sun kalaubalanci hakan, inda suka yi kira da a dage zaman har sai an kammala wani bikin Yaduwa da suke yi a daidai wannan lokaci.

Rikici ya barke ne a lokacin da dubban Falasinawa suka nufi kan iyakokin yankunan biyu, lamarin da dakarun Isra’ila suka ce sun maida martani akan masu jifan su da duwatsu.

Ma’aikatar kiwon lafiya a Falasdinu ta ce dakarun Isra’ila sun yi amfani da harsashi na asali da yaji mai sa kwalla wajen tarwatsa mutane.

Wannan arangama ita ce mafi muni da ta auku a yankin na Gaza da ke cikin yankin Falasadinu, tun bayan yakin 2014 da aka yi tsakanin Isra’ila da Hamas.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG