Mahaukaciyar guguwar nan ta Irma ta fantsamo kan jihar Florida ta nan Amurka jiya Lahadi, ta yi kaca-kace da wannan jaha mai yawan jama'a, musamman ma filin shakatawan nan da ke yamma a gabar kogin Mexico, inda iska ta yi ta kadawa da kara a yayin da kuma ruwa ke ta zubowa da karfin gaske.
Wannan gagarumar mahaukaciyar guguwar ta shafi kusan illahirin Florida, ciki har da birnin Miami da wasu manyan biranen da ke daura da gabar tekun Atlantica; sannan ta dira kai tsaye kan tsibirin nan na Florida Keys kafin ta kada zuwa babban sashin jahar. Sai dai karfin Iskar da ke tafe da guguwar ya ragu sannu a hankali; to amma duk da haka, jami'an ayyukan ceton gaggawa sun yi ta gargadi akai-akai kan yiwuwar guguwar ta sake zaburowa ta yi illa ga mazauna sassa biyu na gabar teku a Florida din.
Rabon wata mahaukaciyar guguwa ta shafi Tampa tun shekaru 100 da su ka gabata.
Jiya Lahadi Shugaba Donald Trump ya dawo Fadarsa ta White House, daga wurin hutawar Shugaban Kasar Amurka na Camp David, inda ya yi ta tarurruka masu nasaba da matsalolin, sannan ya fitar da bayanai dake ayyana mahaukaciyar guguwar a matsayin wani babban bala'i, wanda hakan wani mataki ne na samar da kudi daga gwamnatin tarayya cikin gaggawa.
Facebook Forum