Kamar yadda muka alkawarta maku yau shirin Domin Iyali ya gayyaci wadansu masu ruwa da tsaki a fannin kare hakin bil’adama domin nazarin matakan shawo kan cin zarafin zamantakewa tsakanin iyali da galibi yafi shafar mata da kananan yara. Shirin ya gayyaci Barrister Badiha Abdullahi Mu’azu ‘yar gwagwarmayar kare hakkokin mata da kananan yara, da Malama Naja’atu Bello Jibril malamar tarbiya dake koyarwa a kwalejin nazarin addinin Musulunci ta Aminu Kano, da kuma Mohammed Ali Mashi shugaban kungiyar kare hakin yara kanana da kuma mutane masu rauni da ake kira "Child Protection Network". Wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya fara da neman sanin abinda ake nufi da cin zarafin zamantakewa.
Saurari bayanan wadanda shirin Domin Iyali ya gayyato domin neman hanyar shawo kan wannan lamarin.
Facebook Forum