Gobe laraba kungiyar kwallon kafa ta samari ‘yan kasa da shekara 17 ta Najeriya, Golden Eaglets zata yi karon batta da takwararta ta kasar Australiya, a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya a kasar Chile.
Kwach na Golden Eaglets, Emmanuel Amuneke, yace ‘yan wasan na Australiya ba kanwar lasa ba ne, deomin duk kungiyar da ta kawo wannan gaba a gasar, zata iya lashe wannan kofin.
Amuneke yace tilas su ci gaba da aiki tukuru, su kuma kim tsa ‘yan wasansu tsaf, musamman ganin yadda Croatia ta doke Najeriya a wasan karshe na zagayen farko. A yanzu kuwa, kwaf daya ne, duk kungiyar da aka doke, sai dai ta kama hanyar gida.,
Kungiyar Golden Eaglets ta shigo wannan gasa ta bana a zaman wadda ke rike da kofin na duniya, kuma ta shigo zagaye na biyun a saman rukunin farko da maki 6. Australiya ce ta zo ta uku a rukunin C a bayan Mexico da Jamus. Croatia, wadda ta zo ta biyu a bayan Najeriya a rukunin A, zata kara da Jamus a jibi alhamis.