Wani jariri da aka Haifa bayan sati tara 9 ya bace, bayan wata daya da bacewar jaririn, jami’an ‘yan-sanda sun gano gawar yaron, ana kuma zargin iyayen yaron ne suka yima yaron dukan tsiya, wanda yayi sanadiyar mutuwar shi.
Rahotanni dai na nuni da cewar, tun bayan bacewar yaron, iyayen shi sun sashi cikin gida wanda yayi kwanaki da yawa kamin suka fitar da shi, suka birne shi a cikin wasu itatuwa cikin daji. Yanzu haka dai iyayen yaron zasu fuskanci hukuncin daurin rai-da-rai idan aka tabbatar da abun da ake zargi a tsakanin su.
Maman yaron ta bayyana ma hukumomi cewar, a lokacin da baban yaron ke dukan shi, ta gaya ma baban zai fasama yaron kai, sai yace mata idan batayi mishi shuruba zai hada da ita. Daga baya dai ta fada cewar dalilin da yasa bata kira ‘yan-sanda ba, bayan abkuwar abun shine. Bata so ta rasa mutane biyu da ta fiso a duniya a rana daya. Hakan yasa tayi shuru don rufama mijinta asiri.