Shugaban kungiyar raya Jukunawa ta kasa Mista Bako Benjamin, ya fada a hirarsa da Muryar Amurka cewa suna da shakku kan yadda gwamnatin dake kokawa da rashin kudin biyan albashin ma’aikata da take da su a halin yanzu za ta sake daukar dawainiyar karin albashin mutane 3000.
Da yake kare matsayin gwamnati, kwamishinan ilimi na jihar Taraba Mista Johanes Jigem, ya ce rukuni na malaman da za su dauka za su karantar a makarantun gaba da firamare ne kawai.
Ya kuma kara da cewa babu ma’aikacin gwamnatin jiha dake bin ta bashi na albashi illa ‘yan matsaloli da ake fama da su wajen warware batun albashin malaman firamare.
Dangane da batun daidaita biyan albashin ma’aikata a jihar ta Taraba, duk da tallafin da ta samu daga asusun gwamnatin Tarayya da kuma matakan dakile wawurar kudin da gwamnati ke zargin manyan ma’aikata da aiwatarwa da ta ke dauka, kwamishinan yada labarai Barr. Anthony Danburam, ya ce gwamnati ta gano akwai zagon kasa da ake kulla mata kuma a shirye ta ke ta magance hakan.
Domin jin karin bayani saurari rahoton Sanusi Adamu.
Facebook Forum