Wata gobara da iska ta rura, ta yi sanadin mutuwar daliban makarantar firamare 20 a Jamhuriyar Nijar, kamar yadda jami’an lafiya suka fada a ranar Laraba.
Daliban, wadanda shekarunsu ke tsakanin 7 zuwa 13, na daukan karatu ne a lokacin da gobarar ta tashi da misalin karfe 4:30 (agogon yankin) da yammacin ranar Talata.
Har yanzu a ba a san musabbabin gobarar ba yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike.
Wasu daga cikin ajujuwan da suka kone a cikin ginin makarantar suke, yayin da wasu na rumfuna da ke waje su ma gobarar ta lakume su.
Firai Minista Ouhoumoudou Mahamadou, da ministan cikin gida Alkache Alhada, sun kai ziyara wajen da wannan lamari ya auku inda suka mika jajensu ga iyayen daliban da suka rasu.
Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniyaya UNICEF, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan cikin wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa, “yana aiki tare da hukumomin kasar da sauran abokan hulda don a taimakawa yara da iyalai.”
Labarai masu alaka
Zangon shirye-shirye
-
Nuwamba 04, 2024
Yaushe Ne Bakon Haure Yake Samun Damar Kada Kuri’a A Zaben Amurka?