Kasar Girka da kawayenta na nahiyar turai, sun amince da wani sabon shirin ceto tattalin arzikin kasar a karo na uku, bayan wani taron koli da suka gudanar cikin gaggawa.
A yau Litinin, Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai, Donald Tusk, ya bayyana cewa an samu daidaito na bai-daya a birnin Brussels, bayan sa’oi goma-sha-bakwai da aka kwashe ana tattaunawa.
Kasar ta Girka, ta amince da wasu jerin sharudda masu tsauri, domin ta ci moriyar tayin bashin kusan Dala Biliyan 100, wanda ta ke matukar bukata.
Gabanin kaiwa ga wannan matsaya, Kamfanin Dillancin Labaran Faransa, ya ruwaito wata majiya da ba a bayyana ba, wacce ta ce an samu daidaito tsakanin Firai ministan Girka, Alexis Tsipras, da Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel da Shugaban Faransa, Francois Hollande da kuma Mr. Tusk na kungiyar tarayyar Turai.
Daga cikin matakan tsuke bakin aljihu da Girkan ta amince za ta aiwatar, akwai karin kudaden haraji da za ta yi, da kuma zarftare kudaden fansho.